12 Nuwamba 2019 - 05:14
​Najeriya Na Sa Ran Samun Naira biliyan 543 daga Mai A Shekarar 2021

Fadar shugaban Najeriya ta ce dokar fasalta kasafin ribar hakar danyen man tsakanin gwamnati da kamfanonin hako man, zai samawa kasar karin kudaden shigar da zai kai dala biliyan 1.5, kawatankwacin naira biliyan 543 nan da shekarar 2021.

(ABNA24.com) Fadar shugaban Najeriya ta ce dokar fasalta kasafin ribar hakar danyen man tsakanin gwamnati da kamfanonin hako man, zai samawa kasar karin kudaden shigar da zai kai dala biliyan 1.5, kawatankwacin naira biliyan 543 nan da shekarar 2021.

Gwamnatin Najeriya ta cedokar sake fasalta rabon ribar danyen mai tsakaninta da manyan kamfanonin dake aikin hakonsa a kasar da majalisa ta amince da ita a farkon watan Nuwamban 2019, shi ne sauyi mafi girma cikin sama da shekaru 20, kan yarjejeniyar raba ribar hakon man.

Karkashin sabuwar dokar, dai kamfanonin za su rika biyan gwamnati harajin kashi 10 na jimillar ribar da suke samu a shekara, idan farashin gangar danyen man ya haura dala 20.

A karkashin dokar da aka kafa a 1993, kamfanonin hakar danyen man za su kara adadin kudaden harajin da suke biyan gwamnatin Najeriya, idan farashin gangar danyen man ya zarta dala 20.

Sai dai duk da karuwar farashin gangar danyen man tsawon shekaru, ba a sake yiwa dokar kwaskwarima ba.




/129