3 Nuwamba 2019 - 05:49
Ambaliyar Ruwan Sama Ya Tarwatsa Fiye Da Mutane Miliyan Daya A Gabashin Afirka

Hukumar Agaji ta duniya “Red Cross” ce ta bayyana haka sannan ta kara da cewa; Ruwan da ake yi a yankin ya haura wanda aka saba da shi, kuma cigabansa zai iya kawo cikasa wajen gudanar da ayyukan jin kai da ceto.

(ABNA24.com) Hukumar Agaji ta duniya “Red Cross” ce ta bayyana haka sannan ta kara da cewa; Ruwan da ake yi a yankin ya haura wanda aka saba da shi, kuma cigabansa zai iya kawo cikasa wajen gudanar da ayyukan jin kai da ceto.

Kasashen da ambaliyar ruwan saman ta shafa sun kunshi Somalia, Sudan ta Kudu da Kenya.

Wani dan kasar Somalia ya fadawa manema labaru cewa suna da matukar bukatar taimako a inda suke saboda ambaliyar ruwan wanda ya tarwatsa mutanen da su ka kai dudu dari.

Kungiyar Agaji ta “Action Against Hunger’ ta bayyana cewa; Adadin mutanen da suka bar gidajensu sun haura 180,000 kamar kuma yadda ya lalata amfanin gona.



/129