(ABNA24.com) Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran Ayatullahi Mohammad Ali Mawahedi Karamani ya nuna goyon bayansa game da duk wani yunkuri kawo gyara a kasashen Iraki da Lebanon, a daidai lokacin da ake cigaba da Zanga- zangaa kasashen biyu, saidai ya yi gargadi game da wasu baragurbi dake neman dagula alamura a kasashen biyu.
Limamin ya kara da cewa ya kamata alumomin Iraki da Lebanon su san kimar zaman lafiya da tsaro , kuma su hada hannu da karfe wajen tunkarar makircin makiya dake neman haifar da rikicin kablincitsakanin bangarori daban daban na kasar.
Da yake ishara game da bayanan da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamina’i ya yi, limanin ya ce jagoran ya yi gargadi game damakircin Amurka da kungiyoyin lekan asiri kasashen turai dake samun tallafin kudi daga wasu kasashen larabawa domin haifar da mummunan tashin hankali a kasahen Iraki da Lebanon,ya kara da cewa al’ummomin kasahen suna da hakkin bin hanyoyin da doka ta tanada wajen neman a biya musubukatunsu daga bangaren gwamnati.
Daga karshe limanin ya yi karin haske game da yadda tasirin kasashen waje da cin hanci da rashawa suka yiwajen haifar da tashin hankali a kasashen biyu.
/129
2 Nuwamba 2019 - 06:37
Lambar labari: 985528
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran Ayatullahi Mohammad Ali Mawahedi Karamani ya nuna goyon bayansa game da duk wani yunkuri kawo gyara a kasashen Iraki da Lebanon, a daidai lokacin da ake cigaba da Zanga- zangaa kasashen biyu, saidai ya yi gargadi game da wasu baragurbi dake neman dagula alamura a kasashen biyu.