7 Oktoba 2019 - 05:29
​Mataimakin Firai Ministan Kasar Rasha Yana Ziyarar Aiki A Kasar Venezuela

Mataimakin firai ministan kasar Rasha Yuri Borisov ya isa birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a jiya Asabar don jaddada goyon bayan gwamnatin kasar Rasha ga shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.

(ABNA24.com) Mataimakin firai ministan kasar Rasha Yuri Borisov ya isa birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a jiya Asabar don jaddada goyon bayan gwamnatin kasar Rasha ga shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasar Rasha tana daga cikin kasashen ta suka fi tallafawa gwamnatin Shugaba Maduro tun shekara ta 2006.

Labarin ya kara da cewa kasar Rasha ta bawa kasar Venezuela basussuka wadanda suka kai dalar Amurka billiyon $17 ya zuwa yanzu.

Gwamnatin kasar Amurka da kuma wasu kasashen Laten Amurka suna tababan ingancin zaben da aka gudanar a shekara ta 2018 a kasar ta Venezuela, zaben da shugaba Nicolas Maduro ya lashe da babban rinjaye.

Kasashen Rasha da Cana dai na daga cikin manya-manyan kasashen duniya da suke tallafawa gwamnatin kasar ta Venezuela.

A wani taron hadin guiwa tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu, Ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela ya yabawa gwamnatin kasar Rasha kan tallafin da take bawa gwamnatin kasar Venezuela musamman a cikin irin mummunan halin da kasar take ciki.




/129