(ABNA24.com) Shugaban tawagar tattaunawa na kasar kasar Yemen ya fadawa tashar talbijin din Almayadeen cewa batun sanin fursinonin yaki da muke tsareya kamata ya kasance sirri, saboda hakan zai taimaka wajen musayar fursunonin yaki da kasar Saudiya, kamar yadda kuma ba za mu amince da duk wata yarjejeniya ba, face wadda za ta kawo karshen killacewar da ake yiwa kasarmu, da kuma kawo karshen yaki baki daya.
Muhamad Abdul-salam ya kara da cewa sakonnin kasashen Amurka da Birtaniya na nuni da cewa kasar Saudiya na son dakatar da yaki sai dai har yanzu tana kokwanto, to amma farmakin mai take Nasra daga Allah, babban sako ne ga duk wata kasa da ta yi mamaya ga kasar Yemen, na cewa martaninmu na nan zuwa gare ta.
Abdul-salam ya kara da cewa duk da irin mummunar mu’amalar da aka yi wa fursinoninmu ta hanyar azabtar da su da kuma yi musu yankan rago, a bangarenmu za mu yi kyakkyawar mu’amala da fursunonin makiya har zuwa lokacin da za mu yi musayar fursunoni.
A daren Asabar ne dakarun tsaron Yemen da na sa kai suka kai gagarumin farmaki kan sojojin kasar Saudiya da ‘yan korenta tare hallaka kimanin 500 da kuma kame wasu 2000 na daban.
A Wani taron manema labarai da ya kira, kakakin rundunar sojin Yemen Brigadier General Yahya Sari’i ya ce; adadin sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korensu da su ka kashe sun kai 500, Wadanda kuma suka kama sun haura 2000.
/129
1 Oktoba 2019 - 04:44
Lambar labari: 979467
Shugaban tawagar tattaunawa na kasar kasar Yemen ya fadawa tashar talbijin din Almayadeen cewa batun sanin fursinonin yaki da muke tsareya kamata ya kasance sirri, saboda hakan zai taimaka wajen musayar fursunonin yaki da kasar Saudiya, kamar yadda kuma ba za mu amince da duk wata yarjejeniya ba, face wadda za ta kawo karshen killacewar da ake yiwa kasarmu, da kuma kawo karshen yaki baki daya.