(ABNA24.com) Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin ya kira shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro da ya tattauna da bangaren 'yan adawa domin fitar da kasar daga cikin mawuyacin halin da take ciki.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya ruwaito shugaban Putin na kasar Rasha a wannan laraba na kiran takwaransa na kasar Venuzuela Nicolas Madoro da ya tattaunawa da bangaren 'yan adawa tare da gargadin cewa rashin tattaunawa da 'yan adawa na iya jefa kasar cikin matsala.
Yayin da yake tarbar shugaba Madoro a fadar Kremlin, Shugaba Putin ya jadadda goyon bayansa ga gwamnatin kasar Venezuela sannan ya ce kamata ya yi takwaransa na Venezuela ya bude hanyar tattaunawa tsakanin da bangaren 'yan hamayar kasar.
Putin ya kara da cewa ko shakka babu, gwamnatin kasar Rasha za ta goyi bayan duk wata tattaunawa da za ta kawo ci gaban kasar Venezuela, sannan rashin tattaunawar na iya cutar da al'ummar kasar Venezuela.
Har ila yau shugaba Putin ya yi alkawarin taimakawa kasar Venezuela i da alurar riga kafi na cutar amai da gudawa kimanin miliyan daya da rabi.
A nasa bangare, shugaba Nicolas Madoro ya yabawa Shugaba Putin kan irin taimako da karfin gwiwar da yake baiwa gwamnatin kasar Venezuela, inda ya tabbatar cewa idan suka hada kai za su iya karya dukkunnin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasarsa.
A halin da ake ciki yanzu kasar Venezuela na cikin wani yanayi na matsalar tattalin arziki,sanadiyar karyewar farashin man fetir a Duniya da kuma takunkumin karya tattalin arziki da kasar Amurka ta kakaba mata.
/129
26 Satumba 2019 - 04:25
Lambar labari: 978218
Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin ya kira shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro da ya tattauna da bangaren 'yan adawa domin fitar da kasar daga cikin mawuyacin halin da take ciki.