7 Satumba 2019 - 16:40
Ana Zaman Makoki A Zimbabwe

Shugaban kasar Emerson Manangwawa, ya ayyana zaman makoki na kwanaki har zuwa ranar jana’izar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, wanda ya rasu jiya Juma’a.

ABNA: Shugaban kasar Emerson Manangwawa, ya ayyana zaman makoki na kwanaki har zuwa ranar jana’izar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, wanda ya rasu jiya Juma’a.

Mista Mnangagwa, ya kuma karrama tsohon shugaban da lambar yabo mafi daraja a kasar.

Mista Mugabe ne shugaban kasa na farko da aka taba zaba tun da Zimbabwe ta sami 'yancin kai.

Shuwagabanni da manyan jami’an duniya na ci gaba da aike wa da sakon ta’aziyya ga al’umma da kuma gwamnatin kasar ta Zimbabwe.

A Jiya Juma’a ne aka sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe, yana mai shekaru 95 a duniya, bayan doguwar jinya a Singapore.

.............

300