24 Agusta 2019 - 08:07
Amurka Za Ta Sake Kakabawa Kasar Sin Kudin Fito Na Kasuwanci

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kakabawa kasar Sin sabbin kudin fito akan hajarta ta kasuwanci da take shigar da ita cikin Amurka.

(ABNA24.com) Shugaban kasa ta Amurka Donald Trump ya fada a jiya juma’a cewa zai kara kudin fiton da za su kai dalar Amurka biliyan 75 akan hajar kasar Sin, a matssayin mayar da martani ga Beijing saboda kwatankwacin matakin da ta dauka.

Tun da fari shugaban na kasar Amurka ya yi ishara da yiyuwar kara kudin fiton a kan hajar da kasar Sin din take shigar da ita Amurka, bayan da kasar China din ta yi nata Karin akan kayan da Amurkan take shigar da su cikin kasarta.

Bugu da kari shugaba Donald Trump ya yi kira ga ‘yan kasuwar Amurka da su nemi wata kasa ta daban ba China ba, da za su rika sayen haja daga gare ta, lamarin da ya bai sami karbuwa ba a tsakanin ‘yan kasuwar ta Amurka.

Gwamnatin Amurka a karkashin shugabancin Donald Trump ce ta fara bude yakin kasuwanci da kasar Sin ta hanyar kara kudaden fito akan hajar da take shigar da ita cikin Amurka. Ita ma kasar Sin ta fara mayar da martani akan hakan.
Ana daukar wannan matakin da kasashen biyu suke dauka da cewa zai iya zama barazana ga ci gaba da bunkasar tattalin arzikin duniya.





/129