(ABNA24.com) Shugaban harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya bayyana rashin gamsuwarsa da yanayin da ya sami kansa a kasar Indiya.
Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky wanda ya aika da sako na murya, ya ce; An sa shi a karkashin tsaro mai tsanani ta yadda hatta a cikindakin asibitin da yake ciki da akwai jami’an tsaro masu dauke da makamai.
Har ila yau, Sheikh Zakzaky ya nuna rashin amintarsa da likitocin da za su yi masa aiki, don haka yake cewa:
“Insha Allahu dai gaskiyar magana ita ce akwai bukatar mu koma gida tundadai an yarda mu je wani wuri a waje domin magani tunda India lallai ba ta zama wurin aminci ba yanzu. Sai dai mu koma gida, daman akwai wadansu kasashe da suka yi tayi na cewa za su kar6e mu in mun je. Daga ciki akwai Malaysia da Indonesia da Turkiyua, sai mu je mu tattauna a za6i daya daga ciki sai mu je Insha Allahul azeem. “
Kawo ya zuwa yanzu dai babu mayar da martani da ya fito daga gwamnatin kasar ta Najeriya akan lamarin.
/129
14 Agusta 2019 - 10:01
Lambar labari: 968890
Shugaban harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya bayyana rashin gamsuwarsa da yanayin da ya sami kansa a kasar Indiya.