6 Agusta 2019 - 07:08
​Zarif: Britainia Tana Taimakawa Amurka Wajen Gurgunta Tattalin Arzikin Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Britania ta kwace kataparen jirgin ruwan daukar man fetur na kasar Iran a Jabal Tarik ne don tallafawa Amurka a manufofinta na “ta’addancin tattalin arziki” kan kasar Iran.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Britania ta kwace kataparen jirgin ruwan daukar man fetur na kasar Iran a Jabal Tarik ne don tallafawa Amurka a manufofinta na “ta’addancin tattalin arziki” kan kasar Iran.

Ministan ya bayyana haka ne a jiya litinin a wani taron yan jiridu na ciki da wajen kasar Iran da ya kira a nan birnin Tehran.

A ranar 4 ga watan Yulin wannan shekara ce sojojin kasar Britania suka kwace jirgin ruwan daukar man fetur na kasar Iran mai suna Grace -1 a cikin tekun Medeteranian da sunan jirgin ya sabawa takunkuman da tarayyar turai ta kakabawa kasar Siriya.

Zarif ya kammala da cewa Britania ta fake da takunkuman da tarayyar turai ta kakabawa kasar Siriya ne don kwace jirgin ruwan, amma gaskiyan lamarin tana taimakawa Amurka ne a kan manufofinta kan kasar Iran. Banda haka ministan ya ce kasar Iran ba ta cikin kungiyar tarayyar Turai, ta yaya takunkuman da ta dorawa kasar siriya za su shafita?



/129