(ABNA24.com) Babban Saktaren kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi kawancen Saudiya dangane da ci gaba da kai hare-hare da kuma mamaye kasar ta Yemen.
Tashar Talabijin Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto babban sakataren kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdul-Malik Badreddin al-Houthi a jiya Lahadi na cewa matukar dai kawancen Saudiya ya nace kan ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Yemen da kuma ci gaba da zama a kasar, to babu wani zabi da ya ragewa sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen din face mayar da martani ta hanyar rokoki da makamai masu linzami zuwa kasar cikin kasar Saudiyar.
Al-Houthi ya ce kamata ya yi Saudiya ta faminci cewa sulhu da zaman lafiya shi ne maslaha ga yankin, sannan kuma ya bukaci hadaddiyar daular larabawa da ta gaggauta ficewa daga cikin kasar ta Yemen.
Abdul-Malik Badreddin al-Houthi ya kara da cewa hare-haren baya-bayan nan da Sojoji gami dakarun sa kai na kasar suke kaiwa, ya firgita makiya, kuma muna kara gargadinsu da su guji ci gaba da janyo fitina a yankin, domin a halin da ake ciki yanzu, lokaci ya wuce da makiya za su kawo hari su koma ba tare da an mayar musu da martani ba, duk wani hari da kawancen Saudiyar za su kawo cikin kasar ta Yemen to shakka babu za su fuskanci martani daga Sojoji da dakarun sa kai na kasar ta Yemen.
Tun a watan Maris din 2015 ne kawancen Saudiyar bisa goyon bayan Amurka ya fara kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yemen, lamarin da ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar duban fararen hula da kuma rusa kasar ta Yemen.
/129