Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Aqid Rashad Al-Wutairi, masani kan harkokin soji na Yemen, a cikin wata tattaunawa ta musamman da tashar Al-Masirah ya bayyana: sojojin Yemen sun lalata duk shirye-shiryen kuma sun ƙone duk katunan damarmaki da Saudiyya ke da su na samun nasara ayakinta da Yamen.
Ya ƙara da cewa: sojojin Yemen suna ci gaba da aikinsu na musamman tare da tsaftace faɗin tuddai da ci gaba zuwa Al-Hajriyah, Al-Turbah da Lahj kuma suna ladabtar da Saudiyya da ta sha kashi wanda cikin shekaru goma sha biyu ke ci gaba da mamayewa da killace al'ummar Yemen.
Wannan masanin soji ya yi nuni da cewa: mamayewar Saudiyya yana gudana ne a ƙarƙashin goyon bayan bayanai da kayan aiki na Amurka da Isra'ila da shiru da ko in kula na Larabawa da kasashen Yamma kan kisan kiyashin da ta Saudiyya ke wa al'ummar Yemen kuma abin da sojojin Yemen ke yi, halsatccen kare kai ne daga ikon ƙasa da amincin yankin Yemen.
Al-Wutairi ya bayyana: ayyukan kare kai da hare-haren riga-malam masalllaci, masu ci gaba daidai cikin ƙarfi ana kai su kan maƙiya da tarukansa.
Muna ganin rugujewa da guduwar sojojin hayar Saudiyya; waɗannan ƙungiyoyin da suka kasance suna kashe Yemeniyawa kuma suna yin ɓarna a ƙasa amma abin da ke faruwa a yau, canje-canje ne na musamman da suka ƙaura daga matakin kare kai zuwa matakin kai hari.
Ya nanata: Saudiyya lokacin da ta fara mamayewa, da farko ta kai hari kan filayen jirgin sama kuma tana son nuna yaƙin na Yemen a matsayin yaki ne da ke faruwa tsakinin iya Yamenawa ne kawai, amma daga baya ta nuna ainihin fuskarta tare da kai hari kan wuraren fararen hula cikin tsari kamar hasumiyoyin sadarwa, tankunan ruwa da gadoji amma al'ummar Yemen ba su mika wuya ba kuma martanin sojojin, shi ne kai hari cikin ƙasar Saudiyya. Yanayin ƙasar Saudiyya yanzu yana hannun sojojin Yemen ne kuma hadafofin wurare da ake jefa bamda wuraren, soji da na tattalin arziki na da alaƙa da gwamnatin Al Saud ne.
Al-Wutairi ya ci gaba da cewa: maƙiyiya Saudiyya ta nemi kafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa don dakatar da martanin Yemen da killacewar teku na tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya, amma ta sake gazawa a wannan yunkurin nata kuma da ƙazantantun kuɗinta sun mika hannun roƙon don daukar matakin ƙasa da ƙasa.
Ya yi nuni da cewa: duniya tana mai da hankali ga amincin jigilar ruwa na ƙasa da ƙasa kuma sojojin da jagorancin Yemen sun tabbatar da wannan batu. Amma gazawar Saudiyya wajen samun sabuwar haɗin gwiwa, ya sa ta koma yin ƙarya kan kai hari kan Makka da tunzura takfiriyya don yin aikin takfiranci kan al'ummar Yemen.
Al-Wutairi ya ƙara da cewa: al'ummar Yemen suna sadaukar da mafi kyawun 'ya'yansu don wurare masu tsarki na musulunci, ko a Falasɗinu ko a ƙasar Haramain, kuma suna biyan farashi mai tsanani na daraja da haɗin kan fagen.
Ya nanata: maƙiyiya Saudiyya a yau ta sha kashi a matakin soji, dabarun da bayanai kuma duk katunan damarmaki da ta ke da sun ƙone. Wannan ne ya sa ta kai hari kan wuraren fararen hula.
Al-Wutairi ya roƙi al'ummar Taiz da su haɗu su goyawa sojojin Yemen da jagorancin juyin juya hali kuma ya ce: maƙiyi a yau yaƙinsa yana yi da al'ummar Yemen, ba gwamnatin Yemen a San'a ko sojojinta ba.
Ya yi nuni da cewa: duniya a yau a cikin sojojin da al'ummar Yemen, tana ganin ƙarfin da ba za a iya kayarwa ba wanda ya canza ka'idojin wasa kuma a shirye yake ga kowane zaɓi. Amurka ba ta shiga cikin wannan aiki ba, domin tana sane da jajircewar hare-haren Yemen; musamman da waɗannan sojojin ke da muhimman katuna kamar mashigar Babal-Mandab da Tekun Maliya.
Al-Wutairi a ƙarshe tare da godiya ga rundunar makamai masu linzami ta Yemen ya ce: an zana sabon ma'auni da ya sanya maƙiyiya Saudiyya cikin yanayin tunani kuma ya Sanya ta cikin halayen hauka don neman hanyar fita.
………….
Ra'ayinka