Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wata sanarwa dangane da cikakken ficewar Amurkawa daga Iraki: Korar Amurka daga Iraki, sakamakon dagewar al'ummar wannan ƙasa mai ƙwazo kan 'yancin kanta ne. Al'ummar Iraki tare da tsayin daka na tarihi sun tabbatar da cewa kwazon ƙasa, shine mafi girman makami a gaban ƙwazon masu mulkin mallaka. Nasarar kwazon gwagwarmaya na adawa da mulkin mallaka na Iraki mai daraja kan mamayewar Amurka, wani shafin zinare ne a tarihin neman 'yanci na al'ummomin yankin.
Bismillahir Rahmanir Rahim
"Kuma haƙiƙa maganarmu ta riga ta tabbata ga bayinmu manzanni, cewa lalle su, su ne waɗanda za a taimakawa."
بسم الله الرحمن الرحیم
»وَلَقَدْ سَبَقَتْ کَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِینَ إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ«
Korar yan mamayar Amurka, a haƙiƙa tilastawa ne daga ƙudurin jarumar kasar Iraki kan gwamnatin ta'addanci mai hankoron yaƙi ta Amurka da shugabannin Fadar White House marasa hankali. Amurka wadda koyaushe take magana da harshen ƙarfi, a yau bisa tilastawa ta fice daga ƙasar da ta shafe shekaru ashirin tana mamayewa.
Amurka ta tafi; amma ba da tattaunawa ba, ba da gorin wani abin kirki ba; sao dai bisa ƙoƙarin al'ummar da suka tsaya tsayin daka, da jinin mujahidai da suka ba da rayuwarsu da nufin tsayin daka da ba a taɓa karya ta ba. Yanzu Iraki, cikin Daraja da 'yanci, tana tsaye kan kango na mamayewar shekaru ashirin tana kallon fitowar ranar 'yancin kai.
Babu shakka wannan lamari mai albarka kuma na tarihi shine mataki na farko na neman fansar jinin shahidan Iraki musamman Abu Mahdi Al-Muhandis kuma da yardar Allah ɗaukar fansa na jinin waɗannan ƙaunatattun za a kammala shi da cikakken korar Amurka daga yankin.
Amurka dole ta bar yankin kuma ta bar gudanar da tsaro ga al'ummomin da kansu. Gogewar shekaru ashirin na mamayewa ta nuna kasancewar Amurka ba wai kawai ba ta kawo aminci ba, sai dai ma ita ce asalin mai haifar da rashin tsaro, ta'addanci da rashin kwanciyar hankali a yammacin Asiya. Amurka bayan shekaru ashirin na shiga tsoma bakin soji, tare da kusan mutuwar sojoji 5,000 a cewarta wanda ba ƙididdigar gaskiya ba ce da kashe dala tiriliyan huɗu, an kore ta a cikin kololuwar ƙiyayya da fushin al'ummar Iraki. Waɗannan lambobi, suna nuni da mummunan shan kashi da wulakanci da Amurka ta sha.
Ficewar sojojin Amurka daga Iraki, wani babban lamari ne mai ma'ana na tarihi da gagarumar nasara ga fagen gwagwarmaya. Babu shakka al'ummar Iraki masu ƙwazo tare da ci gaba da wannan yunkuri mai tsarki, za su kawo ƙarshen shiga tsakani na Amurka cikin tattalin arzikin da man fetur na ƙasarsu kuma da haɗin kai da koakrin ƙasa, za su zana makoma mai haske wa kansu. Amurka ba ta taɓa zama abin dogaro mai aminci ba kuma ba ta zama ba; gaskiya da abubuwan da ke faruwa a fagen daga suna bayyana cewa Amurka za ta tafi kuma waɗannan al'ummomi ne ya kamata su gina ƙasashensu.
Da tabbaci ana iya cewa korar Amurka daga Iraki, shine farkon korar su daga duk yammacin Asiya da yankin al'ummar musulmi; Wannan babbar nasara, sakamakon nufin ƙasa na Iraki, jajircewar ƙungiyoyin gwagwarmaya, goyon bayan jama'a da matakan tasiri na gwamnatin wannan ƙasar ne.
Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci a ƙarshe tare da nanata wajibcin hikima da farga na gwamnati da al'umma da dakarun gwagwarmaya na jarumar kasar Iraki a gaban shirye-shirye da fitinu da Amurka da maƙiyan wannan ƙasar za su iya tsara su da don haifar da rashin aminci da rashin kwanciyar hankali a wannan ƙasa mai tsarki; a matsayin 'ya'yan al'ummar Iran, tana bayyananna sanarwa cewa tana ci gaba da kasancewa tare da al'ummomin masu neman haƙƙi da masu adawa da zalunci na yankin don tsaftace yammacin Asiya daga ƙazantattun ragowar mamayewar Amurka da kuma gwamnati mai kashe yara mai nuna wariyar launin fata ta Sahayoniya kuma ba za ta zauna ba har sai an sami cikakken 'yantar da Al-Quds mai daraja.
«وَ لَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا»
"Kuma Allah ba zai taba bawa kafirai wata hanyar nasara kan muminai ba."
Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci
Ra'ayinka