(ABNA24.com) Tashar Talabijin din Rusiya Alyaum ta ruwaito cewa firaministan kasar Libiya Fa'iz Siraj da manzon musaman na MDD Ghassan Salamé sun tattunawa a jiya asabar kan rikicin kasar ta Libiya a gefen taron jana'izar tsohon shugaban kasar Tunusiya marigayi Beji Caid Essebsi.
Gwamnatin hadin kan kasar Libiyan ta ce jami'an biyu sun tattauna kan kokarin da za a yi na ganin an dakatar da hare-haren da dakarun khalifa Haftar ke kaiwa kan birnin Tripoli da kuma komawa kan tebirin tattauna domin magance rikicin ta hanyar siyasa.
A yayin tattaunawar, firaministan hadin kan kasar ta Libiya ya tabbatar da cewa ba za su shiga tattaunawar ba sai bayan da dakarun Haftar sun dakatar da hare-haren da suke kaiwa kan birnin Tripoli, sannan ya ce a mahangarsa, Libiya na bukatar sabon kundin tsarin milka duba da yadda dakarun Haftar ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tripoli.
A nasa bangare Ghassan Salamé ya tabbatar da cewa magance rikicin Libiya ba ya bukatar amfani da karfin Soja, kuma duk wani hari kan fararen hula da gine-gine gari ya sabawa dokokin kasa da kasa na kare hakin bil-adama a mahangar Majalisar Dinkin Duniya, kuma Majalisar na tir da irin wadannan hare-hare.
Abangare guda kuma a daren jiya asabar, jiragen yakin dakarun Haftar sun yi lugudar wuta kan wata asibiti a birnin Tripoli, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutum uku da jikkatar wasu takwas na daban.
/129