23 Yuli 2019 - 04:39
Pakistan : ‘Yar Kunar Bakin Wake Ta Kashe Mutum 6

Rahotanni daga Pakistan, na cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu, a lokacin da wata ‘yar kunsar bakin wake, ta tarwatsa kanta a gaban wani asibiti dake arewa maso yammacin kasar.

(ABNA24.com) Rahotanni daga Pakistan, na cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu, a lokacin da wata ‘yar kunsar bakin wake, ta tarwatsa kanta a gaban wani asibiti dake arewa maso yammacin kasar.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa, harin ya yi ajalin mutum shida da suka hada da ‘yan sanda biyu, a asibitin kauyen Kotlan Saidan, dake gewayen birnin Dera Ismail Khan.

‘yan kunar bakin waken mai kimanin shekaru 28, ta zo wajen ne a kafa, kafin daga bisani ta tarwatsa kanta, inda nan ta kashe ‘yans sanda biyu, da kuma fararen hula hudu, tare da raunata wasu mutane 13 na daban.

An bayyana yankin da mafi fuskantar zubar da jini a wannan kasa ta Pakistan.

Wasu alkalumma da aka fitar sun nuna cewa, an samu saukin matsalolin rashin tsaro masu nasaba da tsatsauran ra’ayi, wanda ya ragu da sama da kasha 80% a cikin shekaru uku na baya bayan nan.

Alkalumman sun nuna cewa mutum 1,131 ne aka kashe a tashe tashen hankula a cikin shekara 2018 data gabata, sabanin mutum 6,574 a cikin shekara 2015.




/129*