(ABNA24.com) Yayin da yake ishara kan yadda gwamnatin Amurka ke kokarin kawar da batun Falastinu a lokacin zaman kwamitin falastinu da ministocin harakokin waje na kungiyar kasashen 'yan baruwanmu a birnin Caracas na kasar Venezuela, Ministan harakokin wajen Iran Muhamad Zavad Zarif ya ce; siyasar bangaranci ta hukumomin Amurka kamar amincewa da birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila da kuma mayar da Ofishin jakadancinta zuwa birnin ya kara rura wutar rikici tsakanin falastinawa da Yahudawa.
Yayin da yake nuna damuwarsa kan yadda wasu kasashen yankin yammacin Asiya ke nuna goyon baya ga bakar siyasar Amurka da gwamnatin yahudawa, Zarif ya kara da cewa shirin Amurka da Isra'ila na yarjejeniyar Karni ba zai taba samun karbuwa ba ga al'ummar Duniya musaman ma al'ummar Palastinu da musulmi baki daya, domin haka babu yadda duniya za ta amince a zartar da wannan shiri, kuma ba zai ci nasara ba.
Zarif ya kara da cewa magance matsalar Palastinu zai tabbata ne kawai ta hanyar kawo karshen mamayar Isra’ila da kuma kafa kasar Palastinu mai cin kashin kanta.
Daga karshe Zarif ya bukaci kungiyar kasashen 'yan ba ruwanmu da su yi tsayin daka domin kalubalantar mummunar siyasar Amurka da Isra'ila ta danniya da kama karya gami da mamaya a duniya.
/129
23 Yuli 2019 - 04:22
Lambar labari: 963584
Ministan harakokin wajen Iran ya bayyana cewa siyasar bangaranci da kuma take dokokin kasa da kasa na gwamnatin Amurka shi ne ya kara rura wutar rikicin Palastinu.