27 Maris 2019 - 18:46
Shin an kama wadanda suka yi garkuwa da Ahmed Suleiman?

Rundunar sojojin Najeriya sun ceto fittacen malamin addinin Musulunci a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

An yi garkuwa da malamin ne a ranar 14 ga watan Maris kan hanyar karamar hukumar Kankara a jihar Katsina da ke arewacin kasar.

Rundunar sojojin Najeriya sun ceto fitaccen malamin kungiyar Izalan nan a Najeriya Alaramma Ahmed Suleiman da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

Sojojin sun bayyana cewa tun bayan garkuwa da malamin, shugaban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai ya ba runduna ta 17 ta sojojin kasar umarnin ceto malamin.

Sojojin sun ce sun yi amfani da dabaru iri-iri da suka hada da tattara bayanan sirri da kuma aiki kafada da kafada da sauran jam'ian tsaro wajen ceto malamin.

Sun bayyana cewa a yanzu haka malamin da sauran malaman da aka yi garkuwa da su na cikin koshin lafiya bayan likitocin sojojin sun duba lafiyarsu.

Har ya zuwa yanzu, babu wani karin bayani kan ko an kama wadanda suka yi garkuwa da malaman ko ba a kama su ba.

Matsalar Garkuwa da mutane ta dade tana ci wa 'yan kasar tuwo a kwarya a fadin kasar.