28 Faburairu 2019 - 16:56
Macky Sall ya sake zama shugaban kasar Senegal

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya lashe zaben kasar da aka yi ranar Lahadi a karo na biyu, inda zai yi shekara bakwai a karagar mulki.

Ya yi nasara a zaben da kashi 58 cikin 100 inda ya fafata da mutum hudu, amma an zarge shi da hana wasu daga cikin abokan hamayyarsa tsayawa takara a zaben.

An hana wasu fitattun mutane tsayawa zaben saboda zarge-zargen cin hanci.

An fara zaben Mr Sall matsayin shugaban kasa ne a shekarar 2012. Ya yi ta yin alkawura gudanar da sabbin ayyuka na abubuwan more rayuwa a yayin neman zabensa.

Ya nuna kansa a matsayin mai son kawo sauye-sauye na zamani, al'amarin da ya bunkasa tattalin arzikin kasar da kashi 6 cikin 100 a shekara daya, daya daga cikin bunkasar da aka taba samu a Afirka.

Sai dai masu suka na cewa yawancin 'yan kasar ta Senegal ba su amfana da wadannan ayyuka ba.