9 Faburairu 2019 - 10:24
Bikini Zagayowar Tunawa Da Ranar 22 Ga Watan Bahman Na Bana Zai Kayatar Fiye Da Shekarun Baya-Cewar Jagora

Jagoran juyin musulinci ya ce a bikin tsagayowar samun nasarar juyin musulinci na bana, al'umma za su fito biyu da na shekarun da suka gabata.

A yayin da yake ganawa da manyan kwamondojin dakarun sama na kasar jiya juma'a, da ya yi daidai da zagayowar ranar mubaya'ar da rundunar sojojin sama suka yiwa Imam Khomeini wanda ya kafa jamhoriyar musulinci ta Iran , jagoran juyin musulinci na kasar Iran Ayatollahi Sayyid Aliyul-Khaminai ya bayyana cewa fitowar al'umma a yayin zanga-zangar ranar 22 ga watan Bahman wato ranar da juyin musulinci ya ci nasara a nan kasar Iran, shi zai karya lagon makiya da kara daukaka al'ummar Iran da tsarin musulinci a Duniya, kuma da yardar Allah fitowar Al'ummar Iran a bana sai ya fi na shekarun da suka gabata.

Jagora ya kara da cewa yayin da ake maganar kare juyi da tsarin musulinci, ranar 22 ga watan Bahman sai ya shigo, a wannan lokaci babu wani babbanci tsakanin al'umma kuma kowa da kowa zai bayyana a dandali domin raya wannan rana mai albarka.

Har ila yau jagoran ya kara da cewa matukar dai tsarin Amurka zai ci gaba da munanan halayensa na zalinci da kuma kuna wutar yaki da gaba a tsakanin al'ummar Duniya, to shakka babu al'ummar kasar Iran za su ci gaba da rera taken mutuwa ga Amurka.

A yayin da yake ishara kan shawarar kasashen Turai na samar da wata kafar musayar kudi da hada-hadar kasuwanci tsakaninsu da Iran domin kare yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiyar kasar ta Iran, jagoran juyin musulinci Ayatollahi Sayyid Aliyul-Khaminai ya gargadi mahukuntan kasar Iran din da kadda suyi dogaro da kasashen Turai.