22 Disamba 2018 - 19:26
ECOWAS na bukatar gaggauta samar da kudin bai-daya'

Kwamatin da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afrika, ECOWAS ta kafa domin lalubo mata dalilin da ya sa kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar ke samun koma-baya, ya bayyana rashin samar da kudin-bai-daya a matsayin babbar matsalar da ke hana cinikayya samun nasara a yankin.

Kwamitin ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya mika wa shugabannin kungiyar a yayin gudanar da taronsu karo na 54 a birnin Abuja karkashin jagorancin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

A yayin zantawa da manema labarai, Ministan Harkokin Wajen Nijar kuma daya daga cikin mambobin kwamitin Kalla Hankurau, ya ce, lallai akwai bukatar gaggauta samar da kudin na bai daya don bunkasa tattalin arzikin yankin.