Baya ga wadanda aka yankewa hukuncin kisan an kuma daure wasu mutane 24 zaman kurkuku na har abada, sai kuma wasu mutane biyar da zaman kurkuku na tsawon shekaru 15.
Kotun ta bayyana cewa an yankewa mutanen hukuncin ne saboda hannun da suke da shi a kisan wani soja ta hnayar dasa bom a garin na Alexandria da kuma tahsin gobara a wata motar da take da alaka da ma'aikatar shari'a.
Gwamnatin Abdulfattah al-sisi ta haramta ayyukan kungiyar ta 'yan'uwa musulmi tun a 2013 da ta hau kan mulki, ta kuma kama da tsare da dama daga cikinsu.