Labanon dai ta yanke shawara cewa wakilinta na dindin-din a kungiyar ne zai halarci taron na yau a birnin Alkahira.
Saudiyya ce dai ta bukaci taron bisa makami mai linzamin na 'yan gwagwarmaya na Houtsi a Yeman da Saudiyya ta cafke a kusa da birnin Ryad a ranar 4 ga watan nan.
Hankulan 'yan siyasa dai a Labanon ya rabu matuka a cacar baki tsakanin kasashen Saudiyya da Iran masu fada a ji a yankin.