16 Oktoba 2017 - 20:29
Alal Akalla Mutane 23 Sun Mutu Saboda Barkewar Sabon Rikici Jihar Flaton Nigeriya

Rahotanni daga jihar Flaton Nijeriya sun bayyana cewar alal akalla mutane 23, wasu rahotannin ma sun ce adadin mutanen ya kai 29 da suka mutu baya ga wadanda suka sami raunuka sakamakon wasu hare-hare da wasu mutane suka kai kauyen Nkiedonwhro da ke karamar hukumar Bassa na jihar a safiyar yau Litinin.

Wasu kafafen watsa labaran Nijeriya din sun ce lamarin ya faru ne a safiyar Litinin lokacin da maharan da ba a riga da an tantance ko su waye ba suka kai harin inda suka kashe mutanen wanda aka ce mafi yawansu mata da kananan yara ne.

Harin na yau dai ya zo ne bayan wasu sabbin hare-haren da wasu yankuna na jihar ya fuskanta lamarin da ya sanya gwamnatin jihar Flaton kafa dokar ta baci a yankunan da hare-haren suka faru, sannan da kuma ba da umurnin a gudanar da gagarumin bincike don gano musabbin sake bullowar irin wadannan hare-hare a jihar ta Flato da ta yi fama da rikice-rikice na kabilanci da na addini.

Kafafen watsa labaran dai sun ce har ya zuwa yanzu Rundunar 'Yan sandan jihar ta Flato ba ta yi karin bayani kan harin ba, to sai dai Kakakin gwamnatin jihar Flato din Emmanuel Nanle ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bankado maharan da suke kai hare-hare a jihar.
...........
300