Majiyar rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan jami'ar Mombasa da ke kudancin kasar a yau Talata, inda suka kashe mata biyu ma'aikata a jami'ar tare da jikkata wasu dalibai masu yawa.
Maharan sun samu nasarar tserewa amma tuni aka nuna yatsar zargin kan mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na kasar Somaliya da suka yi kaurin suna wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan makarantu da jami'o'i a kasar Kenya.