Majiyoyin shari'a sun ce za' a gurfanar da kashin farko na masu zargin kimanin dubu da dari shida cikin makwanni masu zuwa a wasu cibiyoyin tsare mutane a kasar, daga bisani kuma sauren su kimanin 5,000 a yi musu nasu shari'o'in, kuma ko wanne za'a gurfanar da shi, shi kadai muddun dai laifinsa bai da alaka da wani.
Wannan dai shi ne karon farko da za' a yi wa mutane da suka kai irin wannan adadi shari'a kan zargin alaka da kungiyar Boko Haram.
Hukumomi shari'a a kasar sun ce za' a yi zaman shari'o'i ne a cibiyoyin tsare mutanen da ke sassan kasar, maimakon a kotuna.
Kafin hakan dai kungiyoyin kare hakkin dan adam a wannan kasa ta Nijeriya sun dade suna sukar jami’an tsaron kasar da kame fararen hula da sunan ‘yan Boko Haram ba tare da an gurfanar da su a kotu ba..288