4 Nuwamba 2026 - 19:49
Source: ABNA24
Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Zaɓen tsakiyar wa'adi na Majalisar Dokokin Amurka da aka gudanar ranar Talata 3 ga Nuwamba 2026 ya nuna babbar nasara ga jam'iyyar Democrat da kuma shan kashi mai tsanani ga Republicans a manyan jihohin ƙasar. Sakamakon ya mayar da ikon Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ga Democrats, lamarin da ya haifar da martani daga Donald Trump da sauran manyan jami'an jam'iyyun biyu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Bisa ga rahotannin kamfanin dillancin labarai na Associated Press, Reuters da tashar CBS, Democrats sun kwace kujeru da dama na Republicans kuma sun sami ikon Majalisar Dattawa. CBS ta kuma ba da rahoton nasarar Democrats a Majalisar Wakilai da samun rinjaye a wannan majalisar. Wannan shine karo na farko cikin shekaru da Democrats suka mallaki majalisun biyu a lokaci guda.

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru shine nasarar 'yan takarar Democrat a jihohin da a baya suka kasance wuraren da Republicans da Trump ke da ƙarfi. A Texas, James Talarico na Democrat ya doke Ken Paxton na Republican wanda Trump ke tallafawa — nasara ta farko ga Democrats a zaɓen Majalisar Dattawa ta wannan jiha cikin shekaru da dama. Democrats sun kuma sami kujeru a South Carolina, Kansas, North Carolina da Ohio. A zaɓen gwamnonin jihohi ma, Democrats sun sami nasara a Texas inda Gina Hinojosa ta doke Greg Abbott, da kuma a Ohio, Iowa da Georgia.

Martanin Trump

A martaninsa na farko, Trump ya yi ƙoƙarin raba kansa da kashin da Republicans suka sha. A cikin wani saƙo a dandalin Truth Social ya rubuta: "Ba ni ne a kan takardar zaɓe ba kuma da na kasance, da mun yi nasara da babban tazara." Ya kuma zargi Greg Abbott da nisantar ka'idojin Republican. Duk da haka, a cikin tattaunawa da New York Times, Trump ya ce zai karɓi sakamakon kuma yana shirye ya yi aiki tare da Democrats.

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Martanin Shugabannin Democrats

Chuck Schumer, shugaban Democrats a Majalisar Dattawa, ya ce al'ummar Amurka sun zaɓi sauyi kuma ya shaida wa 'yan ƙasa cewa "taimako na zuwa." Hakeem Jeffries, shugaban Democrats a Majalisar Wakilai, ya kira nasarorin a matsayin wani abu da ya wuce nasarar jam'iyya kawai. Jon Ossoff, Sanatan Democrat na Georgia, ya ce mutanen Amurka sun nuna adawarsu ga ayyukan Trump.

Tattalin Arziki Da Yaƙin Iran A Zuciyar Zaɓe

Binciken da aka yi kan masu zaɓe ya nuna cewa tsadar rayuwa ita ce babbar damuwa ga raayuwar yan kasar Amurka. Kusan kashi 48 cikin 100 na masu zaɓe sun ce tsadar rayuwa ita ce muhimmin abu a shawararsu ta zaɓe. Kusan kashi 55 cikin 100 na Amurkawa sun nuna adawa da kuɗaɗen da Trump ke kashewa kan yaƙin Iran, kuma kashi 49 cikin 100 sun ce yanayin kuɗin iyalansu ya tsananta tun Janairu 2025. Wannan ya sa amincewa da Trump ta ragu zuwa kashi 32 cikin 100.

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Musulmin Amurka Sun Yi Karan Icce Kan Trump

Yukunrin da Musulman Amurka da ƙungiyoyin musulunci suka yi na tunkarar Trump ta kasance wani muhimmin ɓangare na zaɓen. Binciken da Majalisar Haɗin Kan Musulmi da Amurka (CAIR) ta gudanar ya nuna kashi 84 cikin 100 na Musulmin da aka yiwa tambaya sun nuna rashin gamsuwa da ayyukan Trump, kuma kashi 72 cikin 100 sun ce za su zaɓi 'yan takarar Democrat. Kashi 89 cikin 100 sun ɗauki matsayin 'yan takara kan Gaza a matsayin muhimmin abu a shawararsu. CAIR ta kuma bayyana cewa a shekarar 2025 ta karɓi korafe-korafe 8,683 masu alaƙa da nuna bambanci kan Musulmai da Larabawa — mafi girman adadi tun farkon tattara irin waɗannan bayanai a shekarar 1996.

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Nasarar Wata Musulma a New York

Darializa Avila Chevalier, wata musulma mai fafutuka kuma mai kare haƙƙin Falasɗinawa, ta sami kujerar majalisar wakilai ta gunduma ta 13 ta New York bayan ta doke 'yar takarar Republican. Wannan nasara ce mai ban mamaki domin ta riga ta doke Adrian Espaillat, wani tsohon ɗan majalisa na Democrat mai ƙarfi, a zaɓen farko na jam'iyyar. Chevalier, wadda aka haife ta a Florida a shekarar 1993 ga iyayen da suka yi ƙaura daga Jamhuriyar Dominican, ta shiga Musulunci a shekarar 2019 ko 2020 bayan ta gwada azumi a watan Ramadan. Ta shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Jami'ar Columbia kuma an kama ta a lokacin zanga-zangar. Ta kasance memba na ƙungiyar "Socialists Democrats of America" kuma tana da alaƙa da Zohran Mamdani, magajin garin New York.

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Martanin Iran

Ismail Baqaei, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Iran, a cikin wani saƙo a X ya yi jawabi ga gwamnatin Amurka: "Girman kai da ɗaukaka share fagen faɗuwa ne." Ya ce kwadayinsu ne ya jawo ƙasarsu cikin mamayewa maras dalili kan Iran. Ya nanata cewa lissafinsu ya ci tura kuma hasashensu ya ruguje saboda ba su fahimci Iran ba kuma ba su fahimci juriya da nufi da daukakar Iraniyawa ba. Ya jaddada cewa "hari kan Iran ba zai kawo nasara ba; shan kashi ne zai same ku."

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Mohammad Baqer Qalibaf, shugaban majalisar shawara ta Iran, shi ya ce al'ummar Amurka sun ce "a'a" ga yaƙin gwamnatin Trump, kuma ya yi gargaɗi cewa duk wani cin amana da sabuwar gwamnatin Amurka za ta yi wa buƙatun al'ummarta domin hidima ga masu cin hanci na ƙasa da ƙasa, zai fuskanci amsa mai tsanani daga Iran.

Rahoto: Yadda Democrats Suka Sami Nasara A Zaɓen Amurka Kan Republicans; Iran Ta Zama Mafarkin Zaɓe Ga Trump

Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Democrats sun ƙarfafa matsayinsu a fagen siyasa na ƙasa yayin da Republicans suka fuskanci raguwar ƙarfinsu sosai. Canjin ikon majalisar zai iya canza ma'aunin ƙarfi a Washington cikin shekaru biyu da suka rage na mulkin Trump, yayin da Democrats ke da ƙarin damar sa ido kan gwamnati da yin tasiri kan dokoki. Tattalin arziki, tsadar rayuwa da yaƙin Iran sun kasance manyan abubuwan da suka shafi qudurin masu zaɓe ga kawo canji, kuma al'ummar Musulmi ta Amurka ta taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan sakamako.

………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha