16 Satumba 2017 - 16:07
Wata Kotu A Masar Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Rai -Da-Rai Kan Mohammad Mursi

Wata kotun koli ta a kasar Masar ta tabbatar da hukuncin daurin rai da rai kan tsohon shugaban kasar Muhammad Mursi

Kamfanin dillancin Labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto wata babbar kotu a birnin Alkahira kan cewa ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan tsohon shugaban kasar Muhammad Mursi tare da laifin aikin leken asiri ga kasar Qatar a cikin kasar.

Labarin ya kara da cewa wannan kotun ita ce ta koli kuma babu daukaka kara a cikin hukuncinta. Dairin rai-da-rai a kasar Masar dai shekaru 25 a gidan kaso.

Banda haka labarin kara da cewa kotun ta tabbatar da hukuncin kisa kan wasu shuwagabannin kungiyar Ikhwanul Muslimin suma kan laifin aikin leken asiri da kuma mikawa kasar Kasar wasu asiran sojojin kasar ta Masar.

Bayan da sojojin karkashin jagorancin Abdulfatah Sisi dai sun yiwa gwamnatin Mohammad Mursi juyin mulki a shekara ta 2013 sojojin sun kama shuwagabannin kungiyar Ikhwanul muslimin da dama sun kuma haramta kungiyar a kasar .