Irin wannan matakin da Amurka dake jagorancin kawancen dake yaki da kungiyar ta IS ta jima tana zawarci, tamakar babban sako ne na nuna hadin kan da ake da shi a yaki da kungiyar, kamar yadda sakatare janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg ya shaidawa manema labarai a birnin Brusels.
Hakan dai na zuwa ne a yayin da ya rage yan sa'o'i kafin babban taron kungiyar ta NATO na yau Alhamis wanda shugaba Donald Trump na Amurka zai halarta a karon farko. 288