'Yan takarar guda 6 wato Hassan Rauhani, Ishaq Jihangiri, Muhammad Baqer Qalibaf, Musatafa Agha Mir Salim, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Hashimi Taba, a jiya sun gabatar da jawabai a tashoshin talabijin daban-daban na kasar Iran.
Dukkanin bayanan nasu suna da alaka ne da irin tsare-tsaren da suke da su a fuskoki daban-daban wajen tafiyar da kasar idan suka samu nasarar lashe zabe.
A yau ne dukkanin 'yan takarar 6 za su sake haduwa wuri guda domin tafka muhawara gaba da gaba a karo na biyu.