Jaridar daily trust ta Nigeria ta bayyana cewa gwamnonin da suka shiga tsakanin sarkin da ganduje sun hada da Aminu bello Masari na Katsina, Ahmad El-Rufae na Kadunua, Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, Kashim Shettima na jihar Borno, da kuma Abubakar Sani Bello na Niger.
Majiyar ta kara da cewa kafin haka gwamnonin sun hadu da Abdullahi Ganduje a Abuja inda suka bukace shi da ya yi watsi da shirinsa na tube sarkin don irin shishshigin da yake masa cikin lamuran shugabancin Jihar.
A ranar Asabar ne gwamnonin suka kira Sarki Sanusi zuwa Kaduna inda suka sasantasu da gwamnan bayan da sarkin ya nemi afwar gwamna Ganduje kan sa in sa da suka yi ta yi a tsakaninsu wanda ya kai ga gwamnatin ya kafa komitin binciken masarautar ta Kano don samun damar tube sarkin.
Bayan sasantawar dai an ga sarki zaune kusa da Gwamna Ganduje a wani bikin daurin aure da aka gudanar a birnin na Kaduna.