Kafofin watsa labarai na Amurka sun ce wani dan-sandan ciki ne ya gano mutumin da ya yi kutsen a fadar Amurka jiya da misalin 12:00 na dare agogon Washington, wato yau da safe a kasashen Afirka.
Rahotannin sun kara da cewa shugaba Donald Trump na cikin gidan a lokacin da lamarin ya faru.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan manufar mutumin ta yunkurin shiga bangaren shugaban kasa a cikin fadar Amurkar.
Ba a kuma yi karin bayani ba kan ko wane ne mutumin.288