Tankokin man guda biyu da aka ajiye su akan hanyar Damboa sun kone kurmus sakamakon aukuwar lamarin.
Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Abdulkadir Ibrahim, ya ce, tuni aka kwashe gawarwakin maharan na kunar bakin wake.
Ibrahim ya ce, an kuma shawo kan gobarar da tashin bam din ya haddasa, yayin da wasu majiyoyi ke cewa, harin bai shafi jama'a ba.288