Ma'aikatar shari'a ta Syria ta ce ko kadan babu kamshin gaskia a wannan rahoto wanda na cin fuska ne ga kasar ta Syria a idon duniya.
Rahoton wanda Amnesty ta fitar ya ce an kashe kimanin mutum dubu 13 a asirce a gidan yarin na Saydaya dake kusa da birnin Damascos.
Rahoton ya kuma ce mafi yawan mutanen da ake kashewa fararen hula ne wanda ake kashewa ta hanyar rataya.288