Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ma'aikatar zata mikawa majalisun dokokin kasar wannan bukatar sannan daga cikin tsarin ma'aikatar Pentagon ce zata horar da sojojin wadan nan kasashe biyu yadda za'a yi amfani da wadan nan makmai musamman jiragen sama daga cikinsu. Jiragen wadanda suka hada da bolom balom suna da kayakin aiki na leken asiri daga sama.
Har'ila yau gwamnatin Amurkan ta kulla yerjejeniya da kasar Kuwait na gabatar da gyagyare wa jiragen yaki masu saukar Ungulu na Apachi wadanda kasar ta dade da sayansu kan kudi dalar Amurka million 400.
A cikin rahoton da ma'aikatar Pentagon ta Fitar, ta sayarwa wadannan kasashe biyu makamai zai kare muradun kasar Amurka a yankin. 288