Yanzu haka dai za a iya cewa komawar sabon shugaban na hannun kungiyar kasashen yammacin Afrika, CEDEAO ko kuma ECOWAS.
Manzon Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Mohamed Ibn Chambas ya bayyana bukatar ganin Adama Barrow ya koma gida a cikin gaggawa, in da ya ce bai dace a samu wani tsawon lokaci ba tare da shugaba a Gambia ba.
Lokaci dai na ci gaba da kwarewa, lura da cewa babu wata rana da aka tsayar a hukumance ta komawar sabon shugaban Adam Barrow.
Manazarta dai na ganin komawar, shugaba Barrow birnin Banjul a cikin gaggawa, shi ne mafi soyuwa.
To amma a cewar Marcel Alain de Souza, shugaban kwamitin gudanarwar Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika, Barrow zai koma gida ne bayan an gama tabbatar da matakan tsaro a birnin na Banjul.288