Ministan Harkokin Wajen na Syria Walid Mu'allim, tare da shugaban hukumar tsaron kasar Syria Ali Mamluk, sun sami tarbar shugaban hukumar tsaron kasar Iran, Ali Shamkhani.
Walidul-Mu'allim ministan harkokin wajen na kasar Syria, ya kuma gana da takwaransa na Iran muhammad Jawad, Zarif inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar ta Syria.
Kasashen Iran da Syrai da kuma Rasha suna da cibiyar tuntubar juna dangane da abind aya ke faruwa a kasar ta Syria.
A halin da ake ciki a yanzu dai an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a kasar ta syria domin bada dama ga bude tattaunawar siyasa.288