Tashar talabijin din Press TV da ke watsa shirye shiryenta daga nan Tehran ta ba da rahoton cewa a safiyar yau ne dakarun bangarorin biyu na suka fara gudanar da wannan atisayen da aka ba shi sunan 'Modafe'en Asemane Velayat 7 (Wato masu kare sararin samaniyyar Wilaya na 7) wanda zai dauki kwanaki uku ana gudanar da shi.
Manufar wannan atisayen dai ita ce hadin gwuiwa da aiki tare tsakanin bangarori daban-daban na dakarun kasar ta Iran a kokarin su na kare sararin samaniyyar kasar daga dukkanin hare-haren da makiya za su iya kawo ta sama.
Ya zuwa yanzu dai an gwada dabaru daban-daban na yaki wajen kare sararin samaniyyar bugu da kari kan wasu sabbin na'urori da suka hada da na'urorin rada-rada masu karfin gaske, bugu da kari kan wasu makamai masu linzami da kuma na'urorin sadarwa da dai sauransu.288