12 Disamba 2016 - 10:08
An kashe babban jami’in ‘Yan Sanda a jahar Rivers

Wasu Yan bangar siyasa a Jihar Rivers dake Najeriya sun kashe Mataimakin Sufritandan 'yan Sanda Alkali Mohammed da mai tsaron sa lokacin gudanar da zaben ‘Yan Majalisun da akayi a karshen mako.

Bayanai sun nuna cewar, wasu zauna gari banza ne suka yiwa Babban jami’in kwantar bauna a Omoku da ke karamar hukumar Onelga inda suka sare kan sa.

Jihar Rivers tayi kaurin suna wajen tashin hankali lokacin zabe, kamar yadda aka gani a zaben shekarar 2015 da kuma zaben cike gurbin da ya kasa kammaluwa saboda hare-haren da suka kai ga kisan jami’in zabe da masu kada kuri’a.288