A jawabinsa a yayin gudanar da shari'arsa a jiya Alhamis: Muhammad Al-Baltaji daya daga cikin shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Ihawan a kasar Masar ya jaddada cewa: Kungiyar 'yan uwa musulmi ta Masar bata da wata alaka da kungiyoyin 'yan ta'addan da suke aiwatar da hare-haren wuce gona da iri a kasar, kuma sanin kowane a tsawon tarihin kungiyar Ihwan basu daukan makami domin aiwatar da ayyukan ta'addanci, iyaka dai sabanin mahanga suke da shi a mahukuntan Masar musamman gwamnati mai ci a halin hanzu.
A fili yake cewa: kungiyoyin da suke dauke da makamai a kasar Masar mafi yawansu a lardin Tsibirin Sina suke, kuma babbar kungiya daga cikinsu ita ce kuniyar Ansarul-Baiti Maqdis da ta yi mubuya'a wa kungiyar taaddanci ta Da'ish.288