Yan uwa musulmi wa’yanda suke a cikin Harka ta Musulunci wadda aka fi sani da IMN.Nine (Shaikh) Hamzah Muhammad Lawal,dan uwanku a cikin addini,dan uwanku a cikin aqida,kuma babban sakatare na Al-Thaqalayn Cultural Foundation,ko kuma Cibiya ta Thaqafa ta Thaqalayn ko kuma Mu’assasa ta Thaqafa ta Thaqalayn.
Na so ne in yi magana daku insha Allah in kuma baku shawara akan wannan maudu’I wanda yake da “hassasiyya” sosai na tabbata gare,wato maudu’in Tattakin Arba’in.Kuma ina so in ce maku akan asasin shawara da nasiha ta yan uwantaka a cikin akida da kuma addini cewa Hikmah tana hukuntawa akan cewa a wa’yannan yanayoyin a yi amfani da “Al-Ahkamuth Thanawiyyah”maimakon “Al-Ahkam Al-Auwaliyyah”,da ma’anar cewa a lura da yanayin da ake ciki a yanzu sai a jinkirta ko dage wannan Tattaki na Arba’in gabaki daya.
Ya kamata mu fahimta a cikin da’irar addini akan cewa shi “Al-Hukmuth Thanawiy” kullum akwaishi,babu lokaci wanda yake babu “Al-Hukmuth Thanawiy .Kawai yana jira ne ya zama cewa ba za a iya dabbaqa “Al-Hukmul Auwaliy” ba sai ya zo shi ya damfaru saboda shi yana yin hukunci ne,wato shi “Hukuma” ne a kowanne lokaci akan “Al-Hukmul Auwaliy”.”Al-Hukmul Auwaliy”a nan wurin yayi kama da “Al-Aslul Amaliy” wanda yake babu lokacin da babu “Al-Aslul Amaliy” ,babu lokaci da yake ba zai dabbaqu ba,kawai yana jira ne ya ga ko kuma yana jinkirta ne “rutbatan” domin yana jira sai a lokacin da ba a samu “Ad-Dalil Shar’iy” wato “Al-Adillal Muhraza ko Muhriz” to shi sai ya zo ya dabbaqu.Wato “da’iman wa abadan” a cikin addinin musulunci wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tsara mana addinin mu musamman mu a Imamiyyah da muke da I’itiqadi babu lokacin da babu hukuncin Allah Subhanahu wa Ta’ala wanda ba ya dabbaqa shi a kowacce irin mas’ala,saboda yanda malaman mu akan asasin karantarwan A’immah da Manzon Allah (sawa) suka rattaba wa’yannan hukunce-hukuncen.
Duk lokacin da “Al-Hukmul Auwaliy” ba zai yiwu ba,akwai “Al-Hukmuth Thanawiy”,wato ba a bar mutane a cikin “faraag” ba.Duk lokacin da babu “Ad-Dalil Muhraza" akwai “Al-Aslul Amaliy” ba a bar mu a cikin faraga ba.Saboda haka wannan yanayi yanayi ne wanda yake-kuma ina da malamai a bayana wa’yanda suke akan wannan,shugabanninmu gabaki daya a cikin wannan addini da kuma a cikin aqida ta Imamiyyah akan wannan ra’ayin-cewa yanzu yanayi ne na Al-Ahkam Ath-Thanawiyyah dangane da ababen da suke faruwa a nan wurin.Saboda haka nasiha ta su jingine wannan tattaki da suke so su yi.Wannan kuma samsam ba tsoro bane,shine “shaja’a” da ainihinta,wannan shine bajinta da ainihinta kuma wannan shine yake nuna cewa mutum yana yin abinshi don Allah Subhanahu wa Ta’ala ba don kanshi ba ko kuma don wani ba.
Na tabbata a wannan abinda nake fadi ko kuma ina kyautata zato sosai akan cewa a wannan abinda na fadi zai yi wahala Malam Muhammad Ibrahim Zakzaky yayi jayayya dani akan haka,zai yi wahala Malam Yaqub Yahya yayi jayayya dani akan haka,zai yi wahala Malam Abdulhamid Bello yayi jayayya dani akan haka,zai yi wahala Malam Adamu Tsoho yayi jayayya dani akan haka,zai wahala da yawa daka cikin ire-irensu suyi jayayya dani akan haka saboda ina kaddara cewa su masu hankali a irin wannan yanayoyin .
Kila wadanda zasu yi jayayya dani ko har ma su fadi bakaken maganganu ko ma har suyi sharri ko suyi zage zage ba zasu wuce kananan yara ba da kuma masu tsuki a cikin kwakwale ba saboda basa fahimta,wadannan ba laifi.Wadancan da ambata daga farko idan tabbas tabbas sun afku a inda nake masu zato cewa ba zasu yi jayayya dani ba.To dayan biyu ina masu nasiha da shawara cewa ko su hana hani yankakke in zai yiwu ko kuma in ba zai yiwu ba su bar’anta itama bar’anta yankakka “alanan” kowa ya san cewa sun yi wannan zai taimaki IMN,zai taimaki shi’anci kuma zai nuna akan cewa daman tun farko ba wai ana yin akan rashin sani ba ko fahimta ko rashin kwakwalwa ba.
Sannan wannan zai bamu dama in Allah ya yarda suka dauki wannan mataki muyi magana da hukumomi a cikin wannan kasar tunda muna da layukan tattaunawa tsakaninmu dasu basu yanke ba,kuma muna kyautata zaton zamu iya zama tare dasu a san yanda za a warware wa’yannan abubuwan.Sannan kuma muna alkawari akan cewa har hukumomin mu na addini wanda muka yi imani dasu muke biyayya gare su suma muna da hanyoyin tattaunawa tare dasu.Zamu iya warware wannan matsalar gabaki daya.Saboda haka wannan nasiha ce “kalisa “da kyakykyawan niyya da kauna da fahimta da kuma son kare jinane.Ban so in shiga cikin dogayen jawabai amma wa’yannan ya kamata a ce su wadatar kuma ina fata za a kyautata min zato.
Wasallallahu Ala Muhammadin Wa Alihid Dayyibinad Dahireen.288
NASIHA DA SHAWARA GA ‘YAN UWA NA HARKAR MUSULUNCI A NIGERIYA(IMN) Daga Maulana Maulana Shaikh Hamzah Muhammad Lawal
13 Nuwamba 2016 - 15:26
Lambar labari: 791700
Yusuf Sulaiman ya rubutu maku A’uzu Billahi Minash Shaidanir Rajeem Bismillahir Rahmanir Raheem Wasallallahu Ala Muhammadin Wa Alihid Dayyibinad Dahireen