Kamfanin dillancin labaran Saumaria News na kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, dakarun Iraki sun kwato kauyuka kimanin 18 daga hannun 'yan ta'addan ISIS da ke kusa da birnin Mausul a cikin sa'oi 48 da suka gabata, kuma suna ci gaba da nausawa.
A nasa bangaren firayi ministan kasar Iraki Haidar Abadi ya mayar da kakkausan martani jiya a kan gwamnatin kasar Saudiyya, dangane da ikirarin da take yi na bayyana 'yan ta'addan ISIS da ke rike da Mausul a matsayin 'yan sunna, inda ya ce abin kunya ne ga masarautar Saudiyya ta fito karara ta bayyana maitarta, a daidai wannan lokaci da duniya ke goyon bayan abin da Iraki ke yi na tsarkake Mausul daga 'yan ta'adda, ya ce yana kira ga Saudiyya da ta bar al'ummar Iraki su zauna lafiya, ta daina daukar nauyin tayar da bama-baman da kisan jama'a a Iraki saboda banbancin mazhaba, inda ya ce rayuwar 'yan takfiriyya na ISIS za ta fi dacewa a masarautar Saudiyya, ba a Iraki ba.288