13 Oktoba 2016 - 12:42
Nigeria: An saki wasu 'yan matan Chibok '21'

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sakin 'Yan matan makarantar Chibok 21 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya ce yanzu haka 'Yan matan 21 na hannun hukumar jami'an tsaron farin Kaya ta DSS.

Garba Shehu ya ce shugaban hukumar Lawal Daura ya yiwa shugaban kasa bayani kan sakin wadda ta biyo bayan tattaunawar da ake tsakanin shugabannin kungiyar Boko haram da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin kungiyar agaji ta Red Cross wadda ke shiga tsakani.

Ana saran Daura ya mikawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo 'Yan matan nan gaba saboda shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Jamus dan kai ziyarar aiki.

Majiyoyi sun ce an saki 'Yan matan ne a musayar da ta shiga tsakanin Fursunonin Mayakan 4 da ke gidan yarin Banki a  arewacin Najeriya da kuma 'Yan makarantar 21.288