28 Satumba 2016 - 17:36
Gwamnatin Amurka Zata Tura Karin Daruruwan Sojoji Zuwa Kasar Iraqi

Gwamnatin Kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata kara tura daruruwan zojojinta zuwa kasar Iraqi don tallafawa ayyukan kwatar birnin Musil daga hannun mayakan kungiyar Daesh.

Kamfanin dillancin Labaran Associated Press daga washington ya nakalto wasu jami'an gwamnatin Amurka suna fadar haka  a yau Laraba. Majiyar ta fadawa Associated Press kan cewa sojojin suna kan hanyarsu ta zuwa kasar Iraqi a halin yanzu, amma bata bayyana adadinin sojojin ba.

Associated Press ta kara da cewa wata majiyar ta shaida masa cewa sojojin zasu kai 600 kuma zasu himmatu da ayyukan horar da sojojin kasar ta Iraqi da kuma bada bayanan sirri ne a aikin kwatar birnin na musil daga kasa ta Iraqi.

Majiyar har'ila yau bata bayyana ko wadan nan sojoji suna daga cikin sojojin kasar na musamman wadanda aka fara aikawa kasar ta Iraqi a watannin baya ba.

Tun shekara ta 2014 ne mayakan kungiyan yan ta'adda ta Daesh ta mamaye arewacin kasar Iraqi, wanda ya hada da birnin Musil birnin mafi girma daga arewacin kasar.288