16 Satumba 2016 - 13:52
Ban Ki Moon Ya Soki Shirin 'Isra'ila' Na Fadada Matsugunan Yahudawa A Yammacin Kogin Jordan

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon,yayi kakkausar suka kan goyon bayan da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila yake ba wa shirin fadada matsugunan yahudawa 'yan share guri zauna a yankunan Palastinawa da suke yammacin Kogin Jordan.

Ban Ki Moon ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a gaban kwamitin tsaron MDD yayin da ake tattaunawa kan batun rikicin Palastinawa da haramtaacciyar kasar Isra'ilan inda ya ce ko shakka babu ci gaba da gina matsugunan yahudawa wani lamari ne da ya saba wa dokokin kasa da kasa kuma haramun ne don haka wajibi ne a kawo karshensa'

Har ila yau kuma Ban Ki Moon ya kiyaye firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ilan Benjamin Netanyahu da ya san cewa shirin fadada matsugunan yahudawan da kuma kara fadada haramtacciyar kasar Isra'ilan a matsayin wani  haramtaccen shiri.

Wannan dai ba shi ne karon farko da MDD ta ke sukan irin wannan shirin ba, to amma yahudawan suna ci gaba da shi sakamakon daurin gindin da suke da shi daga manyan kasashen duniya.288