7 Yuni 2016 - 17:33
Turkiyya : Bom Ya Kashe Mutane 11 A Santambul

Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane 11 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 36 na daban sun raunana a wani harin bom a birnin Santambul.

Wadanda suka rasa rayukan su a harin sun hada da 'yan sanda bakwai da kuma fararen hula hudu.

Bayanai sun nuna cewa an tayar da bom din ne daga nesa a unguwar Beyazit a daidai lokacin da wata motar bas dake daukeda 'yan sanda kwantarda tarzoma ke wucewa.

Turkiyya dai ta jima tafa fama da hare-hare da mahukuntan kasar ke dangatawa ga 'yan jihadi da kuma 'yan tawayen Kurdawa na PKK.288