Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, bayan zantawar da ta yi da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah a daren Litinin da ta gabata, yahudawan Isra'ila suke ci gaba da bayyana firgicinsu kan barazanar da ya yi.
Masana da masu sharhi a Isra'ila, sun bayyana a kafofin yada labarai suna bayyana barazanar da Sayyid Nasrullah ya yi kan tarwatsa duk wasu muhimman wurare a kowane sako na Isra'ila, matukar ta kai hari a Lebanon da cewa, abin da ya fada da gaske ne, kuma Hizbullah tana da karfin da za ta yi hakan a halin yanzu, lamarin da ya jefa firgici da tsoro a cikin zukatan yahudawan Isra'ila maras misiltuwa.288