Bama baman sun fashe ne da misalin karfe 10 na safe a agogon kasar a yankin Sultanahmet kusa da Blue Mosque.
Wani bayani da aka wallafa a shafin intanet na gwamnan birnin ya ce mutane 15 ne suka jikkata.
Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar-bakin-wake ne suka tayar da bama baman ko da ya ke ba a tabbatar da rahotannin ba.
'Yan sanda sun killace wurin da lamarin ya faru.288