Sakataren Ma’aikatar tsaron Amurka Ashton Carter ya ce tattaunawarsu na yau zai mayar da hankali ne kan hanyoyin kawar da matsala a hare-haren da bangarorin 2 ke kaiwa kan mayakan ISIS a Syria
Carter ya ce duk da dai suna bayyana shakunsu kan Rasha, ganawar ya zama tilas domin gudun karo da juna.
Tattaunawar Amurka da Rasha na zuwa ne, bayan rahotanni a yanzu na bayyana tasirin da harin Rasha ke yi kan ISIS sama da wanda Amurka da kaweyanta ke kaiwa kasar sama da shekara 1.
Ko a yau sai dai gwamnatin Moscow ta sanar da kaddamar da sabbin hare-hare 40 a yankin Aleppo, Idlib, Latakia da Dier Ezzor kan mayakan.
Sai dai har yanzu Amurka na jadada cewa harin Rasha ba yana zuwa kan ‘yan ta’ada ba ne. 289