Tun a ranar Assabar ne girgizan kasar mai karfin maki 7.8 ta abkawa kasar Nepal inda ta rusa gidaje a Kathmandu tare da lalata hanyoyin ababen wa da katse hanyoyin sadarwa.
Yanzu haka kayan agaji sun fara isa kasar daga kasahsen duniya yayin da dubban mutane ke ci gaba da kwana a sararin Allah saboda rashin matsuguni.
Muhimman bukatun ‘yan kasar sun hada da ruwan sha da abin da zasu ci da magani da kuma jakar ledar sanya gawarwaki.
Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Laxmi Prasad Dhakal ya ce adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwar su ya kai 4,310, yayin da ake cigaba da neman wasu da gine gine ya rubta da su.
Jami’in ya kuma ce mutane 7,953 suka samu raunuka
Kasar Amurka ta ce zata aikawa Nepal agajin Dala miliyan 10 a matsayin agaji don tallafawa mutanen da girgizar kasar ya ritsa da su.
Ma’aikatar tsaron kasar ta kuma umurci zaratan sojojinta 24 da ake kira Green Beret, wadanda ke kasar da su taimakawa hukumar agajin gaggawa wajen ceto wadanda hatsarin ya ritsa da su.ABNA