Firaministan Italiya Matteo Renzi ya ce kawo yanzu an sami gawarwakin mutane 28.
Rahotanni sun ce hadarin ya faru ne yayin da mutanen wadanda suke makare a kwale kwalen kamun kifi suka karkata gefe daya na kwale kwalen suna kokarin darewa wani babban jirgin fasinja da ya doso.
Kasar Italiya na jagorantar gagarumin aikin ceto wanda ya hada da jiragen ruwa a shirin da kuma jiragen sama. ABNA